Tirkashi: Wani Dalibin jami’a ya lakadawa malamarsa duka kawo wuka daga neman taimako

Kwara – Wani ɗalibi dake karantar kwas ɗin Microbiology a jami’at Ilorin, (UniLorin) ya lakaɗawa lakcaransa dukan kawo wuka.

Dailytrust tace Ɗalibin mai suna, Captain Walz, bai samu yin kwas ɗin neman sani makamar aiki ba (SIWES), dan haka yaje neman taimakon lakcaran.

Rahotanni sun bayyana cewa lakcaran da abin ya shafa, Mrs Zakaria, ita ce zata kula da ɗalibin yayin da zai yi Project a 400 level.

Hakanan kuma an tabbatar da cewa Walz ya lakadawa malamar tasa dukan tsiya ne ranar Alhamis din nan da ta gabata.

Meyasa abin ya kai da duka?

A binciken da muka yi, dalibin ya je har ofishin malamar domin neman ta taimaka masa, saboda bai samu damar yin SIWES ba kwata-kwata.

Amma da lakcaran da nuna ƙin amincewar ta, nan take Walz ya fusata, ya lakaɗawa malamar dukan tsiya wanda yasa ta ji raunuka a jikinta.

Bugu da ƙari, ba’a ɗauki dogon lokaci aka kawo mata ɗauki kuma aka garzaya da ita asibiti domin kula da lafiyarta.

Wane mataki jami’a ta ɗauka?

Daraktan hulɗa da jama’a na jami’ar, Mr Kunle Akogun, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai ta wayar salula ranar Asabar da daddare.

Daraktan hulɗa da jama’a na jami’ar, Mr Kunle Akogun, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai ta wayar salula ranar Asabar da daddare.

Yace:

“Eh tabbas lamarin ya auku, amma lakcaran tana yanayi mai kyau, kuma tuni mataimakin shugaban jami’ar (VC). Farfesa Abdulkareem Age da wasu malaman jami’a suka ziyarci lakacaran da lamarin ya shafa.”

“Jami’a baki ɗaya bata ji daɗin abinda ya faru ba, kumazata tabbatar da an yi adalci. Sannan kuma ya roki a kula da lafiyar malamar yadda ya dace ta asusun jami’a.”

A wani labarin kuma

Source: Legit Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button