Cristiano Ronaldo ya shiga Al Nassr na Saudiyya har zuwa 2025

Cristiano Ronaldo ya shiga kulob ɗin Al Nassr na ƙasar Saudiyya kan wata yarjejeniya da zai ba shi damar zama har shekara ta 2025.
Kaftin ɗin na Fotugal ya kasance babu igiyar kowa a kansa bayan ya bar Manchester United sanadin wata hira da ya yi mai cike da taƙaddama inda ya soki lamirin ƙungiyar.
An ba da rahoton cewa Ronaldo zai riƙa karɓar albashi mafi tsoka a tarihin ƙwallon ƙafa wato fam miliyan 177 a shekara.
Ɗan ƙwallon ma shekara 37 ya ce “ya ƙagu ya taka leda a wani sabon fagen ƙwallon ƙafa na wata ƙasar daban”.
Al Nassr – kulob ne da ya zama zakara a gasar Saudiyya na Pro League har karo tara – ya bayyana cimma yarjejeniya da Ronaldo a matsayin “wani kafa abin tarihi”.
Kulob ɗin ya ce matakin zai “zaburas da gasar ƙwallon ƙafarmu, da ƙasa da kuma zuri’a mai tasowa, yara maza da mata za su kasance masu son yin fice a rayuwarsu”.
A ƙarshen kaka, Ronaldo ya yi fatali da kwanturagin fam miliyan 305 daga wani kulob ɗin ƙasar Saudiyya – Al Hilal – saboda a lokacin yana farin ciki da zamansa a Man United.
Tun farko a watan Nuwamba, ɗan wasan gaban ya faɗa a lokacin wata hira da Piers Morgan don shirin TalkTV inda ya ce yana jin tamkar United ta “ci amanarsa”, kuma ba ya ganin mutuncin kocin ƙungiyar Erik ten Hag abin da ya tilasta ficewar dagakulob ɗin.
Ronaldo, wanda ya ci ƙwallo 145 a wasa 346 da ya buga wa Man U, ya bar Juventus zuwa kulob ɗin Old Trafford a watan Agustan 2021 – shekara 11 bayan ya tafi zuwa Real Madrid.
Wata bakwai ya rage a cikin kwanturagin da yake ɗaukar fam dubu 500 duk mako a Man United sai dai tafiyar da ya yi nan take “ta samu amincewar duk ɓangarorin biyu”.
Kwana ɗaya bayan ya bar ƙungiyar, sai aka haramta masa buga wasa biyu a cikin gida saboda ya tankwaɓe wayar salula a hannun wani mai goyon bayan kulob ɗin Everton bayan an cinye United a filin wasa na Goodison Park a watan Afrilu.
Hukuncin zai yi aiki a kansa a duk wani sabon kulob da ya shiga – a Ingila ne ko a ƙasashen waje – duk da yake matakin bai shafi harkokin kulob na nahiya ba kamar Gasar Zakarun ƙungiyoyi.
Kwanan nan Ronaldo ya koma gida daga Gasar cin Kofin Duniya da ya buga wa ƙasar Fotugal a Qatar, inda ya kafa tarihi ta hanyar zama mutum na farko da ya ci ƙwallo a Gasannin cin Kofin Duniya biyar da ƙwallon da ya ci Ghana a karawar farko.