Iyayen Daliban Da Suka Makale A Ukraine Suna Neman Dauki

Iyayen daliban Jihar Taraba da suka makale a kasar Ukraine, sun roki Gwamnatin Tarayya da kungiyar Tarayyar Afirka da su dauki dukkan hanyoyin diflomasiyya don kwaso ‘ya’yansu zuwa gida Najeriya.

Daya daga cikin iyayen Yakubu David, ya koka kan yadda ’ya’yansu da ke kasar Ukraine suna karatu, an tilasta musu yin kaura zuwa iyakar Ukraine da Poland amma an kasa barin su shiga Poland din.

David, ya kara da cewa suna tuntubar ’ya’yansu amma halin da suke ciki ya bukaci gwamnatin tarayya da kungiyar Tarayyar Afirka da su dauki matakin gaggawa domin a kwashe su da sauran dalibai daga Afirka zuwa mafaka.

Ya ce abin takaici ne yadda aka ji cewa dalibai daga Afirka sun makale duk da cewa an bar wasu ‘yan kasar su tsallaka zuwa Poland.

David ya kara da cewar, sun damu da tsaron yaran ganin yadda yakin da ke tsakanin Ukraine da Rasha ke kara ta’azzara a kowace rana.

Tuni dai wasu daga cikin ‘yan Najeriya da wasu bakaken fara daga Afirka da suka makale a Ukraine sun koka kan yadda ake nuna musu wariyar launin fata.

Kazalika sun koka kan yadda mahukuntar Najeriya suka kai musu dauki a kan lokaci har sai da yaki ya barke tsakanin kasashen biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button