Buhari Zai Tafi Landan Ganin Likita

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai tafi birnin Landan da ke Birtaniya domin ganin likitocinsa na tsawon mako biyu.

Kakakin Shugaban, Femi Adesina ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa ranar Talata, inda ya ce Buharin zai wuce Landan ne bayan halartar wani taro a kasar Kenya.

Ya ce Shugaban zai bar Abuja ranar Talata domin halartar taron Shirin Majalisar Dinkin Duniya a Kan Muhalli (UNEP) karo na 50, wanda za a yi tsakanin uku zuwa hudu ga watan Maris din 2022 a birnin Nairobin kasar Kenya.

Femi ya ce Buhari zai halarci taron ne bayan Shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta ya gayyace shi.

A cewar kakakin Shugaban Kasar, Buhari, yayin tafiyar, zai samu rakiyar Ministan Harkokin Waje na Najeriya, Geoffrey Onyeama, da Minista a Ma’aikatar Muhalli, Sharon Ikeazor, da mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya), da Shugaban Hukumar Leken Asiri ta Najeriya, Ambasada, Ahmed Rufa’i Abubakar, da kuma Shugabar Hukumar da ke Kula da ’Yan Najeriya Mazauna Kasashen Waje, Abike Dabiri-Erewa.

Yayin taron na Kenya dai, ana sa ran Buhari zai gabatar da jawabi kan matsayin Najeriya a harkar kare muhalli, kamar yadda ya zo daidai da taken taron na bana.

Ana sa ran taron zai duba kalubalen muhalli a duniya cikin shekaru 50 din da suka gabata bayan kafa hukumar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button