Hausa Novels

BAƘAR WASIƘA Part 1

Sponsored Links

ASH MULTIMEDIA TV wata manhajar youtube channel ce da ta kware wajen iya karanta Hausa Novels wanda mutane da dama suke dam barwa wajen sauraran duk wani sabon Hausa Novel daya fito. Wanda yanzu haka zaku dinga iya samun sabbin videos din wannan channel a blog din mu mai suna HausaDrop.Com ayi sauraro lafiya.

BAƘAR WASIƘA Part 1: Hausa Novels 2022

GABATARWA.

Related Articles

BAƘAR WASIƘA…

Mai farin rubutu

Idan aka ce Bakar Wasika Mai Farin Rubutu. Ana nufin wani dunkulelen sako mai wuyar fassara, kamar mutum mai nagarta sai wani mummunnan kaddara ta fada masa.

Ban ce tafiyar mai sauki ba ce.

Ban muku alkawarin zallar soyayya ba.

Ban ce babu farincikin ba.

Kunci, bakinciki da damuwa, sune abubuwan da suka taru suka tare farincikin AMINATU, kalubalen rayuwa bayan wata rayuwar, tabbas akwai kuka akwai damuwa da bakinciki.

Labarin Tafida, Rafi’a, Laila, Madina, Ramlee, Faruk, Amal, Kabir da kuma Aminatu.

Labarin BAKAR WASIKA. Labari ne da zai tabo wani bangare na rayuwar mace, kuma wani bangare na rayuwar al’ummarta da iyayenta…

Ina fatar zaku karbe shi kamar sauran, duk kuwa da na san ba lallai ne yai muku dadi ba domin ba soyayya ce zalla ba, kalubalen rayuwa ne da fadi tashin yar gudun hijira!

A ina zata kwana? Wa zai bata masauki? Taya za a fahimce ta har a nade mata damuwarta? Wa zata kaiwa kukanta iyeyenta ko al’ummarta? Ta ina mafarkinta ke tabbatuwa? Ashe bayan wuya akwai wata wuyar, bayan dadi ma akwai wata wuyar, bayan wuya kuma akwai dadi.

Tabbas akwai ciwo a rayuwar da baka san karshenta ba, akwai tsoro a mafarkin da ka gagara farkawa! Ta ina lamarin ya fara? Ina tsakiyarsa da karshe? Yaushe damuwar zata wuce? yaushe bakincikin zai gushe? Sai yaushe hawayen zasu tsaya? Zuwa yaushe ne kuncin zai yanke?

Ashe a cikin rayuwa akwai wata rayuwa? A cikin rayuwar ma akwai mutuwa?

Domin jin darussan dake cikin wannan labarin ku kela channel namu mai suna ASH MULTIMEDIA dake manhajar Youtube don jin ya zata kaya a labarin. Muna godiya.

https://www.youtube.com/watch?v=lq63Hqn7BO0

Kasance da HausaDrop.Com domin samun sabbin wakokin hausa ko kuma naija music dan samun nishadi a rayuwa.

hausadrop

Aminu B Yusuf, Editor in Chief at HausaDrop.Com

Leave a Reply

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button