El-Rufai ya ce ƙona dazukan arewa ne kawai zai yi maganin ɓarayin daji

Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya bayar da shawarar a ƙona dazukan arewa domin ƙakkabe ɓarayin daji da suka addabi yankin.

“Na sha faɗa cewa, abin da ya kamata shi ne a ƙona dajin, a kashe su gaba ɗaya, daga baya mu sake shuka bishiyoyi,” kamar yadda gwamna El-Rufai ya shaidawa kafar Arise TV a wata hira ta musamman.

Ya ƙara da cewa ƙona dajin ne kawai mafita duk da matakin zai shafi waɗanda ba su ji ba su gani ba.

“Ya fi a kakkabe su a dawo da zaman lafiya mutane su koma noma,” in ji shi.

Ya ce yadda ake tunkararsu ba zai kawo ƙarshen matsalar ba – “domin idan an kore su daga Sokoto, za su tsere su tsallaka Kebbi.”

“Abin da za a yi kawai a yi masu ruwan wuta ta sama da ƙasa a dukkanin jihohi shida na arewa maso yammaci da Neja.”

“Idan aka yi haka ina ganin cikin makwanni ana iya maganin matsalar ”

Source: Bbc Hausa


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button