‘Yadda Nake Kai ’Ya’yana Daji ’Yan Bindiga Suna Lalata Da Su’

An cafke wata matar aure da take kai ’ya’yan cikinta da na ’yan uwanta wurin ’yan bindiga a cikin daji inda suke yin lalata da su.

Matar ta bayyana yadda take kai wa ’yan bindiga ’ya’yan nata da ’ya’yan ’yan uwanta ne bayan da rundunar ’yan sanda ta musamman kan yaki da ’yan fashin daji da ’yan ta’adda sun samu nasarar cafke ta tana tsaka da wannan aika-aika.

Wakilinmu ya ruwaito cewa matar tana yi wa ’yan bindigar safarar ’yan mata zuwa Dajin Galadimawa ana aikata alfasha da su.

Rundunar ’yan sandan ta IRT wadda Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya ya kafa, ta titsiye matar inda ta bayyana yadda son zuciya ya rufe mata idanu ta shiga wannan harka.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button