Rayuwar Zawarawa ’Yan Kannywood Sai Hakuri – Mansurah Isah

Mansurah Isah

Tauraruwar fina-finan Kannywood, Mansurah Isah, ta ce kalubalen da mata ’yan fim da aurensu ya mutu ya wuci yadda ake zato, duba da irin mawuyacin halin da suke shiga da mummunan zargi da mutane ke musu ba tare da sanin hakikanin dalilin rabuwar auren nasu ba.

Mansurah, wadda ita ma aurenta da tauraron Kannywood, Sani Danja, ya zo karshe a kwanakin baya, ta ce babu matar da za ta so fitowa daga gidan mijinta, alhali suna zaman lafiya da sanin darajar juna.

A wannan hirar da muka yi da ita, ta bayyana irin abubuwan taikaici da ake wa mata ’yan fim da sauran matan aurensu ya mutu, da kuma yadda ita kanta ta tunkari nata kalubalen.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button