Idan har Rarara na raye kamata yayi ya fito yayi wakar zuwan mai hula Lagos – Sheikh Bello Yabo

Fitaccen Malamin addinin Musuluncin nan Sheikh Bello Yabo ya caccaki shahararren mawakin siyasar nan na Arewacin Najeriya, Dauda Kahutu Rarara, sakamakon shiru da ya fito yayi a wannan lokaci da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yiwa ‘yan Arewa laifi.

Malamin ya ce a lokacin mulkin PDP na Goodluck Jonathan, Rarara ya sha yin wakoki na cin mutunci kan yadda Jonathan ke tafiyar da mulkin shi a wancan lokacin, inda a lokacin mutanen Arewa dadi suka dinga ji suna yaba masa, sai dai a wannan karon kuma da abin ya dawo kan shugaba Buhari yayi shiru da bakin sa.

Malamin ya bayar da misali da cewa a lokacin da bam ya tashi a Abuja lokacin mulkin na Jonathan, Rarara fitowa yayi ya gabatar da wata waka mai suna “Zuwan Mai Malafa Kano”, Malamin ya ce idan har Rarara na nan a raye bai mutu ba kamata yayi ya fito yayi wakar zuwan “Mai Hula Lagos”.

Idan ba a manta ba dai a lokacin mulkin Jonathan na PDP bam ya tashi a Nyanya cikin birnin Abuja, inda a lokacin maimakon shugaban kasar yaje yayi jaje a wajen da lamarin ya faru sai ya dauki kafa ya tafi Kano wajen karbar tsohon gwamnan jihar ta Kano Malam Ibrahim Shekarau, wanda ya canja sheka a lokacin zuwa cikin jam’iyyar PDP.

Wannan abu da ya faru ya jawo kace-nace matuka a lokacin hakan ya sanya fitaccen mawakin ya fito yayi wakar “Zuwan Mai Malafa Kano”, wakar da tayi suna sosai a wancan lokacin.

Malamai da dama dai sun fito sun nuna rashin jin dadin su da kuma Allah Wadai da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari kan yadda ya nuna halin ko in kula da kashe-kashen dake faruwa a yankin Arewa.

Kudi talakawa suka dinga tara maka don ka samar musu da saukin rayuwa, yanzu ka nuna littafi yafi rayukan su daraja – Sheikh Nuru Khalid

A wani bidiyo da aka dauka a wajen Tafrin fitaccen Malamin nan mai kokarin ganin an samar da zaman lafiya a fadin Najeriya, da kuma ganin an samu hadin kai tsakanin Musulmi da Kiristoci, wato Sheikh Muhammad Nuru Khalid, ya bayyana takaicin sa dangane da yadda shugaban kasa Muhammad Buhari da sauran shugabannin Najeriya suka dauki rayuwar talaka tamkar ta dabbobi.

Malamin ya bayyana cewa a lokacin zabe talakawa ba wai iya kuri’u kawai suka jefawa shugaban kasar ba, har kudi suka dinga cirewa daga aljihun su suna tura masa domin a lokacin suna da yakinin zai dan sama musu saukin rayuwa, amma sai labari ya sha banban.

Sheikh Nuru Khalid ya ce Najeriya kasa ce da Allah ya halitta ba tare da neman taimakon kowa ba, haka kuma dukiyar dake kasar ya ajiyeta ne domin al’ummar kasar, dan haka babu dalili da zai sanya a dinga kashe al’umma a kowacce rana, ga kuma bala’in wahalar rayuwa da al’umma ke ciki ba tare da shugabanni sun dauki wani mataki ba.

Haka Malamin ya nuna takaicin shi kan kone mutane da aka yi a cikin mota a jihar Sokoto, inda ya ce bai kamata shugaban kasa ya san da wannan lamari ya dauki kafa ya tafi jihar Lagos tallar littafi ba.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button