Sanatan jam’iyyar APC Uba Sani ya maidawa tsohon sarkin kano Sunusi martani kan cewa tattalin Nageriya ya kusu durkushewa

Sanatan jam'iyyar APC Uba Sani ya maidawa tsohon sarkin kano Sunusi martani kan cewa tattalin Nageriya ya kusu durkushewa

Sanata Uba Sani a musanya abin da wasu ke fada akan tattalin arzikin kasa Nageriya, Uba Sani ya bayyana cewa tattalun arzkin kasar ta Nageriya bai sami kurkure ba, sannan kuma yayi kira da abaiwa CBN hadin kai.

Sanatan dake jihar Kaduna ya yaba da kokarin da ake yi sannan kuma ya fadi cewa, a dai na bata sunan kasar Nageriya.

shugaban kwamatin da yake kula da harkokin banki inshora da kuma hukumomin tattalin arziki na majilista, sanata Uba Sani, yayi magana kan tattalin arzikin kasar nan.

A ranar lahdi uku 3 ga watan oktoba shekara ta 2021, sanata Uba Sani ya shaidawa manema labarai cewa, a halin yanzu tattalin arzikin kasar Nageriya bai kama hanyar da zai rushe ba.

kamar yadda Leadership tayi rahoto a lokacin da yake wannan jawabin, Uba Sani yayi kira ga al’umma da su dai na kashewa kasar ta Nageriya kasuwa.

Sanata Uba Sani wanda shike wakiltar jihar Kaduna ta tsakiya a majilistar dattawa yayi gargadi kan cewa, yawan sukar da akewa bankin CBN yana taba tattalin arzikin kasar Nageriya.

A cewar Uba Sani ana bukatar a yarda da aiyukan babban bankin kasar Nageriya CBN, sannan kuma a nemi hadin kai ga masu zuba hannun jari a kasashen waje, sanatan ya bayyana cewa shugaban majilistar dattawa, Dr Ahned Lawan, ya bukaci kwamutocinsu da su bawa gwamnati dukkan wata gudun mawa da take bukata.

haka kuma ‘yan majilistar zasuyi iya bakin kokarin su na ganin an farfado da darajar Naira da tattalin arzikin kasar Nageriya ta hanyar tallafawa babban bankin kasa CBN, da kuma duk wasu ma’aikatun gwamnati.

Sannan kuma jaridar ta kara yin rahoto kan cewa, sanata Uba Sani ya bayyana cewa duk kokarin da gwamnan bankin CBN zai yi, dole kowa ma ya tashi tsaye domin ganin an farfado da tattalin arzikin kasar Nageriya.

Sanata Uba Sani ya kara da cewa, babban bankin CBN yayi abin da ya kamata a yaba masa wajan bada tallafin covid-19 domin hana tattalin arzikin kasar durkushewa sakamakon mummunar annobar.

Ub Sani ya kara da cewa, A yanzu ana cikin wani hali sannan ana bukatar a dauki matakin farfado da tattalin arzikin Nageriya, bazamu shiga sahun masu ganin laifin wasu ba sai dai mu bada gudun mawa.

Bayamin na sanata Uba Sani yazo ne a dai dai lokacin a akaji tsohon gwamnan babban bankin Nageriya CBN, Muhammad Sunusi II yana cewa tattalin arzikin kasar Nageriya ya kusa durkushewa.

Muhammad Sunusi II tsohon sarkin jihar Kano ya tabbatar da cewa kasar da take yiwa Nageriya kwai ita ma ta kusa shekawa lashira, sannan kuma ba wannan ne karo na farko da Muhammad Sunusi ya II ya fadi irin hakan ba.

Kalli wannan bidiyon bake kasa


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button