Za A Fara Daure Masu Yi Wa Mata Kaciya Shekara 4 A Jihar Edo

Gwamnatin Edo ta gargadi mazauna Jihar cewa masu yi wa mata kaciya za su iya fuskantar hukuncin daurin shekara hudu a gidan gyaran hali.

Kwamishiniyar Walwalar Jama’a da Harkokin Mata ta Jihar, Misis Maria Omozele Edeko, ce ta yi gargadin a karshen mako a Benin, babban birnin Jihar, yayin bikin ranar yaki da yi wa mata kaciya ta duniya.

Ta ce sashe na 11 na Kundin Dokar da ya Hana Cin Zarafin Dan Adam (VAPP), ya tanadi hukuncin daurin shekara hudun ga duk wanda aka samu da aikata laifin.

Dokar, wacce aka kirkira a 2021, na neman kawo karshen kowanne irin cin zarafin mutane da kuma hukunta masu hannu a ciki.

Kwamishiniyar ta ce, “A matsayinmu na Jiha, za mu bi diddigin matsalar tun daga tushe ta hanyar ziyartar yankunan da suke yi wa mata kaciya don mu fadakar da su a kan illar yin hakan, da kuma sanar da su hukuncin da doka ta tanada.”

Ta ce gwamnati za ta karfafa alakarta da sauran masu ruwa da tsaki zuwa yankunan karkara don wayar musu da kai.

Misis Maria ta kuma ce, “Lokaci ya yi da zamu kawo karshen yi wa mata kaciya. Akwai hukuncin daurin shekara hudu ga duk wanda aka kama da hannu wajen yi, tamakawa a yi, goyon baya ko kuma iza wutar yi.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button