Yawan Shan ‘Paracetamol’ Na Iya Haddasa Ciwon Zuciya – Bincike

Wani bincike da aka gudanar ya gano cewar yawan shan kwayar magani ta Paracetamol ga masu ciwon hawan jini, na iya haifar musu da ciwon zuciya da kuma shanyewar barin jiki.

A cewar binciken, wanda wasu masu binciken a Jami’ar Edinburg da ke kasar Scotland suka gudanar, sun ce maganin na iya zama barazana ga masu cutar kuma likitoci ya kamata su rage ba su maganin.

Amma sun jaddada cewa shan maganin saboda ciwon kai da zazzabi ba shi da wata illa.

Masanan sun ce sun gano akwai bukatar gudanar da bincike duba da yadda masu ciwon hawan jini ke faman shan maganin a kodayaushe don rage musu radadi.

Ana yawan amfani da Paracetamol a fadin duniya saboda ciwon kai ko ciwon jiki na dan takaitaccen lokaci, amma kuma ana iya amfani da shi ga ciwuka masu tsanani na tsawon lokaci.

Kazalika, wani bincike da aka gudanar a shekarar 2018 ya gano cewar cikin shekara guda, akalla mutum miliyan daya aka rubutawa maganin na Paracetamol a lokacin da suka ziyarci asibiti.

Bincike ya gano cewar yawan shan maganin na iya ta’azzara ciwo ga masu hawan jinin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button