’Yan Kannywood Sun Goyi Bayan Sheikh Daurawa Kan Zargin Aibata Mata

A makon jiya ne fitaccen malamin addinin Musulunci nan, Sheikh Aminu Daurawa ya yi wani bayani a wani karatunsa kan gudun duniya, inda a ciki ya yi batun cewa al’aurar mace ba zai yiwu ta fito da shi fili tana yawo a bude ba duk son shi da maza ke yi, inda ya yi nuni da yanayin rashin kyan ganin shi.

Maganar ta Shehin Malamain ta tayar da kura a kafafen sadarwa, inda wata wadda aka ce jarumar fim ce mai suna Maryam Ishak ta ragargaji malamin a wani faifan bidiyo da ta fitar.

Sai dai binciken Aminiya bai gano yadda ta zama jaruma ba, domin Aminiya ba ta samu gano wani fim da ta fito ba, kuma ba a samu wata alakarta da fim ba.

Maganar Maryam ta bar baya da kura, inda aka yi ta ce-ce-ku-ce a kafafen sadarwar zamani a tsakanin masu kare ta da masu zagin ta.

Ba a bar Masana’antar Kannywood ba a wajen batun, inda fitaccen furodusa, Alhaji Sheshe ya bude fili da wani dogon rubutu, inda a ciki ya caccaki Maryam.

Alhaji Sheshe ya ce, “Muna Allah-wadai da kalaman wannan shaidaniyar a kan Malam Aminu Daurawa. Malam mene ne hukuncin masu zagin wani malami?

“Hukunci na farko Annabi (SAW) ya ce mutuwar malami mutuwar dukkan halittu ne hatta abin da ba ya motsi kamar bishiyoyi saboda muhimmanchin malamai ya sa Annabi (SAW) ya fadi haka.

“Annabi ya ce wani lokaci yana nan zuwa da al’ummata za su raina malaman kirki su watsar da su suna musu kallon banza sai Allah Ya jarrabe su da masifu uku.

“Za su yi ta yin sana’a babu albarka. Ma’ana ba wai babu samu ba, amma za ka ga mutum nemansa na karuwa wahalarsa da dogon buri suna yi masa yawa ba ya da hutun da talaka yake da shi hatta matarsa ba ta da lokacinsa. To wannan arzikin babu komai cikinsa sai wahala saboda an cire albarka a ciki.

“Allah zai rika ba su shugabanni azzalumai marasa tausayin talakawa kuma su rasa yadda za su yi da su.

“Za su rika mutuwa a Musulunci amma suna cikawa babu imani saboda talauci ya sa su sabon Allah barkatai… Allah Ya sa mu dace Ya ganar da mu hanya madaidaiciya.”

Shi ma jarumi Ali Nuhu ya yada wani rubutun da darakta Nura Mustapha Waye ya yi, inda a ciki yake cewa, “Duk wanda ya san martabar addini, ba zai zagi malaman addini ba, saboda su ne suke koya mana bin Allah da ManzonSa.”

Tuni ake cewa Hukumar Hisbah tana neman Maryam bisa kalaman nata ga Sheikh Daurawa, duk da cewa Aminiya ba ta samu tabbacin haka ba.

A wani bangaren kuma, an fara cewa ta nemi yafiyar Shehin Malamin kan cin zarafinsa da ta yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button