’Yan Fashi Sun Kashe ’Yan Sanda, Sun Wawushe Kudi A Motar Daukar Kudi

’Yan fashi sun kashe mutum hudu, ciki har da ’yan sanda biyu sannan suka yi awon gaba da kudin da ke cikin motar daukar kudi ta banki.

Kwamishiniyar ’Yan Sandan Jihar Oyo, Ngozi Onadeko, ta ce ’yan sandan biyu  sun rasu ne a sakamakon harbin su da aka yi a wuya.

A lokacin da ta ziyarci wurin da abin ya faru, Onadeko ta kara da cewar ’yan sandan sun kashe daya daga cikin ’yan fashin, amma maharan sun tafi da gawar.

Rahotanni sun bayyana cewa motar kudin da ta taso daga titin Iwo, ’yan fashin sun tare ta ne a kan hanyar Idi-Ape, inda suka rika harbi kan mai uwa da wabi.

Ganau sun ce, ’yan fashin sun zo wurin ne a cikin wata farar mota, inda suka yi amfani da karfi wajen balla motar kudin, sannan suka yi awon gaba da kudin da ke cikinta.

Aminiya ta gano cewa mutane da dama sun jikkata a lokacin harinn a yankin Idi-Ape da ke Ibadan, a ranar Alhamis.

Sai dai kwamishiniyar ta ce an baza jami’an tsaro a fadin jihar don tabbatar da cewar ’yan fashin ba su sulale daga jihar ba.

Ta kara da cewa tuni rundunar tare da hadin gwuiwar sauran hukumomin tsaron da ke jihar suka tsunduma bincike don gano inda barayin suka shiga.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button