’Yan Bindiga Sun Sace Hedmasta A Neja, Sun Bukaci A Basu N100m

Advertisement

’Yan bindiga sun sace Hedmastan wata makarantar firamare da ke Karamar Hukumar Mashegu ta Jihar Neja, tare da neman a biya su Naira miliyan 100 a matsayin kudin fansarsa.

Hedmastan makarantar wacce ake kira da Jigawa, dai an dauke shi ne tare da wani mutum a yankin.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa wakilinmu cewa ’yan bindigar, wadanda suka shafe kwana biyu suna cin karensu ba babbaka a kauyen tun ranar Juma’a, sun tafi da mutanen zuwa wani kauyen.

Majiyar ta ce iyalan daya mutumin sun yi tayin biyan Naira miliyan biyar domin fansar dan uwan nasu, amma ’yan bindigar suka ki amincewa.

Ya kuma ce har yanzu masu garkuwar ba su fara tattaunawa da iyalan Hedmastan ba tukunna.

Ya ce, “Iyalan Hedmastan sun shaida musu cewa dan uwansu malamin makaranta ne, ba shi da kudi, amma suka ce wannan bai shafe su ba.

“Wadanda aka fara yin garkuwa da su ranar Juma’a, daga bisani aka sako su bayan biyan kudin fansa sun shaida mana cewa sun gane fuskokin wasu daga cikin masu garkuwar.”

Akalla kauyuka biyar ne da ke Karamar Hukumar ta Mashegu ’yan bindigar suka kai wa hari, inda suka kashe mutum biyu tare da sace dabbobi da dama.

Source: Aminiya Dailytrust

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button