’Yan Bindiga Sun Kashe DPO Da Soja A Katsina

Advertisement

’Yan bindiga sun kashe wani soja da kuma baturen ’yan sanda a wani sabon hari da bata-tarin suka kai a Jihar Katsina.

Maharan sun kai farmakin ne a garin Magamar Jibia da ke Karamar Hukumar Jibia ta jihar inda suka yi wa DPO mai suna DSP A. A. Rano da sojan kwanton bauna suka kashe su.

Aminiya ta gano cewa DOP din ya jagoranci karin jami’an tsaro ne da ke kan hanyarsu ta mara wa takwarorin baya a yaki da ’yan bindiga, lokacin da maharan suka yi musu kwanton bauna suka kashe shi da sojan.

Wani mazaunin yankin, Muhammad Aminu, ya ce maharan sun kuma ji wa wani babban hafsan soja mai mukamin Kanar rauni, sannan suka yi awon gaba da mutane da dama a harin.

“Sun yi wa jami’an tsaro kwanton bauna sanna suka bude wa motar da DPO din Jibia da sojan suke ciki wuta.

“Shi kuma Kanar Masoyi, an harbe shi a cinya, yanzu ana duba lafiyarsa a asibiti,” a cewar Aminu.

A baya, DPO din Jibia da wasu sojoji sun fatattaki ’yan bindiga a kauyen Daddara da ke Karamar Hukuma Jibia inda aka kashe wani basarake da wasu mutum biyar.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya wallafa hoton ta’aziyyar mamatan a kafafen sadar da zumunta, amma bai yi bayani a hukumance ba zuwa yanzu.

Hukumomin ’yan sanda a Jihar Katsina sun bayyana cewa wasu jagororin ’yan  bindiga, kamar Abdulkarim, Dan Karami, Dangote da Abu Rabe sun dawo kauyen Tsambaye da ke Karamar Hukumar Jibia bayan sojoji sun matsa musu da gragargaza a jihohin Sakkwato da Zamfara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button