Yajin Aiki: Buhari Ya Roki ASUU Ta Tausaya Wa Daliban Najeriya

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya roki Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa ASUU da ta tausaya wa dalibai ta janye yajin aikin da take yi a halin yanzu.

Shugaban yayi wannan roko ne ranar Alhamis a taron ci gaba na kasa da ba da Lambar Yabo ga fitattun ’yan Najeriya da kungiyoyi da ke hukumomin gwamnati da masu zaman kansu ta karfafa guiwar masu kirkirar ta kasa da aka gudanar.

Buhari ya kuma rarrashi daliban da su kara hakuri, inda ya ce gwamnati za ta yi amfani da dan abin da ke asusunta ta magance koke-koken na ASUU.

A wata sanarwa da Shugaba Buharin ya fitar mai dauke da Sa hannun kakakinsa, Femi Adesina, ya ce ya ba wa Shugaban Ma’aikata, da Ministan Kwadago, da na Ilimi, da na Kudi, da na Kasafi da Tsare-tsare umarnin zama da masu ruwa da tsaki domin biya wa da kungiyoyin bukatunsu.

Da Shugaban ke bayani kan taken bikin na bana “Cim ma kololuwar kirkira bisa tsarin ingantaccen Ilimi,” yayi alkawarin gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa wajen inganta tsarin ilimi a kasar nan.

Kazalika, ya ce gwamnatinsa na sane da cewa ci gaban kowacce kasa ya ta’allaka ne da ci gaban iliminta, don haka madamar kasar nan na son a dama da ita a duniya sai ta ba wa tsarin iliminta muhimmanci fiye da komai.

Haka kuma Buharin ya ce babu yadda za a yi bangaren tattalin arzikin kasa ya bunkasa bayan bangaren ilimi na durkushe.

Ya ci gaba da cewa domin karfafa guiwar matasa su shiga aikin koyarwa, ya sanya gwamnatinsa ta maida lokacin ritayarsu daga shekaru 60 na haihuwa zuwa 65, yayin da shekarun aiki kuma suka tashi daga 35 zuwa 40.

Haka kuma ya ce ya bada umarnin fara amfani da sabon tsarin albashi ga malaman firamare da sakandare, da suka hada da alawus na musamman ga wadanda aka tura makarantun karkara da na kimiyya, hadi da biyan albashi da karin matsayi akan lokaci.

A nasa bangaren Ministan Kwadago, Chris Ngige, ya ce tun sanda aka kirkiri wannan lambar girmamawar a 1991, An bawa mutane 382, da kungiyoyi 97.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button