Yadda wani ango ya fatattaki amaryar sa bayan ya gano cewar ba budurwa ba ce watanni 4 bayan auren su

Wani dan Najeriya ya yanke igiyar auren sa da amaryar sa bayan da ya gano cewar amaryar tasa ba budurwa ba ce. Kamar yadda labarin yazo a shafukan sada zumunta, mutumin ya fada tarkon amaryar tasa ne inda ta nuna masa fa ita cikakkiyar budurwa ce ashe abin ba haka bane.

Yarinyar ta kasance mai hankali

Ko da yake wanda ya yada labarin a shafin Twitter shima ya bada shaidar cewa yarinyar tana da hankali, sai dai angon ya kasa daurewa bayan ya gano irin karyar data shimfida masa kafin auren su.
Tuni dai aka mayar wa mutumin kudaden da ya kashe a lokacin hidimar auren.

Ga yadda sakon yazo a shafin twitter:

@ChukwuSomma ya rubuta: “Wata ‘yar unguwarmu an maida kudin auren ta sannan kuma an kwaso kayanta zuwa gidan mahaifinta saboda karyar da ta yi wa mijinta cewa ita budurwa ce, auren watan shi 4 kacal ….ashe har yanzu maza na wannan abun?? Omo!”

Kadan daga cikin martanin masu amfani da shafin twitter

@FunmiKolz ya ce: “Me ya sai bayan wata 4 sannan zai korota gidan iyayenta?”

@MEzulike ya ce:”to ita meyasa zatayi karya, shi mutumin dole sai budurwa ne ya ke nema saboda abin ya,kullemin kai.

@sakwaofkigali ya ce: “A gaskiya abin ya burge har mijin ya iya zama da ita har wata 4 Hakan ya kara nuna yadda matar ta kasance maƙaryaci shi kuma mutumin ya kasa ci gaba da hakuri Budurwa.”
Tabdi dama mata har yanzu suna wannan karyar? Shikuma mijin da ya,yi hakuri ya yafe mata sai dai kuma idan akwai wata matsalar bayan wannan.”

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button