Yadda Mutane Suka Yi Tara-Tara Wajen Kama Wata Mai Yunkurin Satar Dalibi A Kano

Wata mata da ba a kai ga gane ta ba ta fada hannu bayan da ’yan sa-kai da jama’ar unguwar Koki da ke birnin Kano suka yi tara-tara wajen kama ta, lokacin da take kokarin sace wani yaro mai shekara biyar a kan hanyarsa ta zuwa makaranta.

Yaron, mai suna Bashir Jamilu, dalibi ne a aji biyu na nozire a makarantar Ulumiddin da ke Koki.

Mahaifiyar dalibin, Aisha Salisu Koki, ta shaida wa Aminiya cewa ta tura yaron makarantar ne wajen misalin karfe 8:30 na safe, inda ya ci karo da matar a kan hanyarsa, wacce ta ce zata je mayanka ne don sayo nama da taliya da madara, amma yaron ya fara kuka.

Ta ce, “A daidai Lungun Barebare ya fadi a kasa, inda ta ja shi a kasa a kusa da makarantar. Ya nemi ta kyale shi ya shiga makarantar, amma ta ki, ta ce za ta dawo da shi, dalilin ken an da ya sa hankalin mutane ya zo kanta, har suka fahimci me ke faruwa.

“Da mutane suka titsiyeta, sai ta ce musu danta ne, nan take suka fara dukanta, saboda sun san karya take yi.

“Ina zuwa wajen na tarar da ita tana ja-in-ja da mutane a kan sai ta tafi da shi wai danta ne.

“Tana gani na ta fara kawo min duka tana tambayar wai ni na haife shi, shi kuma dan ya fara kuka yana kiran ‘Ummata’.

“Daga nan ne na karbe shi na karasa da shi makaranta, ita kuma ’yan sanda suka dauketa daga wajen ’yan sa-kai zuwa ofishin ’yan sanda na Jakara.

Ta ce daga nan ne kashegari aka aike da su zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuffuka (CID) na Rundunar ’Yan Sanda, inda su kuma suka kai ta sashen yaki da garkuwa da mutane.

Matar ta kuma jinjina wa yunkurin ’yan sa-kai na unguwar, wadanda ta ce da taimakonsu ne aka samu nasarar kubutar da yaron daga hannun matar.

Ko da yake Aisha ta ce yanzu haka matar tana CID tun ranar Alhamis, amma da wakilinmu ya tuntubi Kakakin ’yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce har yanzu babu cikakkun bayanai a kan lamarin, amma zai tuntube shi daga bisani in ya samu.

Source: Aminiya Dailytrust

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button