Yadda Angon ’Yan Mata 8 Ke Rayuwa Cikin Annashuwa

Labarin wani mai sana’ar zanen Tattoo a kasar Thailand ya dauki hankalin jama’a sosai a Intanet bayan da aka bayyana cewa, yana zaune ne a gidansa tare da matansa takwas duk ’yan mata da ya aure su a kusan lokaci guda.

Angon mai suna Ong Dam Sorot, matashi ne mai zanen Tattoo da ya kware a zanen gargajiya na ‘yantra’ na asalin addinan Indiya, kwanan nan ya gana da wani fitaccen dan wasan barkwanci na kasar Thailand don yi hira game da matsayin aurensa mai cike da ce-ce-ku-ce.

Sorot, ya auri mata takwas, dukkansu da suke zaune a gida daya kuma suna daukar kansu a matsayin iyali mai farin ciki da zaman lafiya.

Tattaunawar wadda aka sa a shafin Youtube, zuwa yanzu ta samu ra’ayin jama’a sama da miliyan 3 a shafin.

Ong Dam Sorot ya gabatar da kowace daga cikin matansa tare da bayyana yadda suka hadu. Matan takwas dai sun bayyana mijin nasu a matsayin wanda ya fi kowa kirki, mai kula da al’umma, kuma sun yi ikirarin samun rayuwa mai ban-mamaki.

Angon ya hadu da matarsa ta farko, Nong Sprite a wurin bikin wani abokinsa ne kuma cikin sauri ya nemi aurenta.

Ta biyu mai suna Nong L, ya hadu da ita a kasuwa, sai Nong Nan, matarsa ta uku sun hadu a asibiti.

Matansa na hudu zuwa na shida sun hadu ne a shafukan sada zumunta na Instagram da Facebook da TikTok. Sai matarsa ta bakwai, Nong Film, sun hadu ne bayan ya gan ta a lokacin da ya ziyarci wajen bautar gumaka na Phra Pathom Chedi tare da mahaifiyarsa, yayin da matarsa ta takwas kuma ta karshe, Nong Mai ya hadu da ita yayin hutu a birnin Pattaya tare da matansa hudu.

“Watakila shi ne mutumin da ya fi kowa kulawa da muka taba gani,” matan takwas duka sun yarda da shi.

Ya kara da cewa yana mu’amala da su sosai har ba su da wani abu da za su yi jayayya ko gardama a kai.

Biyu daga cikin matan Sorot suna da juna biyu a yanzu, kuma yana da da tare da matarsa ta farko, Nong Sprite.

Matan suna kwana a dakuna hudu, biyu a kowane daki, kuma suna jiran lokacinsu don raba kwanciyar aure da mijinsu.

A bayyane yake, babu wanda ke da matsala da tsarin mijin. Da yake magana a karon farko Ong Dam Sorot ya ce lokacin da ya kawo yiwuwar auren mace ta biyu, Nong Sprite ta ce, tana sonsa matuka kuma ta yarda da aurensa, musamman da yake a koyaushe yana mai da hankali kan tambayar ta ko ta gamsu da ra’ayinsa.

Ta ce, ta yarda muddin ya kawo matarsa ta biyu gida, ita ce za ta fara karbarta. Su kuma matan bakwai da suka amince su aure shi sun san cewa yana da aure, yawancinsu kawai sun ce, suna matukar soyayya da shi kuma sun yarda da lamarinsa.

Mutum ne kyakkyawa, mai hankali kuma ya tabbatar da cewa zai iya kula da su.

Duk da cewa, wadansu daga cikin matan sun samu matsala wajen bayyana wa iyalansu cewa, suna auren miji mai mace fiye da daya, ba su yi kasa a gwiwa ba a kan auren Ong Dam, kuma a karshe abokansu da iyalansu sun amince da lamarin.

A yayin tattaunawa da Ong Dam Sorot ya ce, ya shaida wa matansa cewa su kasance masu gaskiya a koyaushe. Idan sun samu wani abu da ba su gane ba su zo su fada masa.

Yana tambayarsu sau uku idan sun tabbata suna son rabuwa da kowa sai shi, idan suka amsa ‘eh’, sai su kasance tare. Har yanzu wani abu na rabuwa bai faru ba.

Ong Dam, wanda yake da shahararren shafinsa na sada zumunta da kuma tashar YouTube, ya ce a kullum mutane suna tunanin cewa, shi mai kudi ne kuma yaya zai iya kula da iyalansa, amma ya ce ba gaskiya ba ne.

Kowane dan gidansu yana da aikin da ya rataya a wuyansa, kuma matansa suna samun abin da ake ajiyewa ta hanyar yin ayyuka, ko sayar da kayayyaki daban-daban, tun daga abinci zuwa kayan kwalliya da kayan aikin hannu.

Sai da tsarin rayuwar aure na Ong Dam Sorot ya haifar da zazzafar muhawara a shafukan sada zumunta, inda wadansu suka nuna jin dadinsu ga mai zanen da ya hada zaman gidansa da matasansa takwas, yayin da wadansu kuma suka nuna masa cikin zolaya cewa ‘ba mace daya ba, amma mata takwas!’

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button