Yadda Ake Cin Zalin Daliban Najeriya Da Suka Makale A Ukraine

Daliban Najeriya da sauran baki da suka makale a kasar Ukraine bayan barkewar yaki sun koka kan yadda jami’an tsaron kasar suke cin zalinsu da nuna musu wariyar launin fata a kan iyakokin kasar.
Wata daliba daga Najeriya, Rachel Onyegbule, da ke karatun aikin likita a Ukraine, ta ce jami’an tsaron kasar sun tilasta mata tare da sauran dalibai da suka fito daga kasashen Afirka sauka daga wata bas a wani shingen bincike a iyakar kasar da Poland, suka sa motar ta wuce da ’yan kasar Ukraine zalla.
“Muna kallo manyan bas sama da 10 suka zo suka wuce suka bar mu; Mun yi zaton idan sun gama kwashe ’yan Ukraine za su dauke mu, amma jami’an suka ce sai dai mu taka a kasa, motoci sun kare, babu mai daukar mu.”
Racheal wadda ke shekararta ta farko a jami’ar da ke Lviv ta ce haka suka ci gaba da tsayuwa a cikin matsanancin sanyi a garin Shehyni mai nisan mil 400 daga Kiev, babban birnin kasar Ukraine, daga baya suka taka zuwa kan iyakan.“Jikina ya yi tsami ban jin komai saboda tsananin sanyi, kwananmu hudu babu barci. A ko’ina ana fifita ’yan Ukraine a kan ’yan Afirka maza da mata. Ba sai mun tambaya ba, mun san dalili. Mu yanzu gida kawai muke so mu koma,” a cewar Racheal.
Ta bayyan hakan ne ta wayar tarho a lokacin zantawarta da kafar yada labarai ta CNN, ranar Lahadi a lokacin da take kokarin tsallakawa zuwa kasar Poland daga Ukraine.
A karshe dai a ranar Litinin da misalin karfe 4.30 na asuba, dalibar ta samu sahalewar shiga Poland.