Yadda Aka Kashe Mutum 220 A Kwana 17 A Neja

Akalla mutum mutum 220 ne aka kashe a Jihar Neja a cikin kwana 17 da suka gabata a sabuwar shekarar da muke ciki.

Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani-Bello ya ce daga shiga Sabuwar Shekarar 2022 zuwa yanzu an kashe fararen hula 165, jami’an tsaro 25, da kuma ’yan banga 30 a jihar.

“Mun samu rahoton an kai hare-hare 50, ’yan bindiga sun mamaye kauyuka 300 an yi garkuwa da mutum 200, cikinsu har da ’yan kasar China mutum biyu.

“Sannan an kuma kashe jami’an tsaro 25, fararen hula 165 da ’yan banga 30,” duk dai daga ranar Sabuwar Shekara zuwa ranar 17 ga watan Janairun da muke ciki.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, bayan ganawarsa da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba.

Sai dai bai bayyana alkaluman ’yan bindigar da aka kashe a tsakanin lokaci ba, amma ya bayyana kwarin gwiwa cewa yanayin tsaron jiharsa zai inganta a cikin mako biyu masu zuwa da jami’an tsaro za su yi aikin taron dangi.

“Duk da cewa a halin yanzu ba za a iya kawar da matsalar gaba daya ba,” inji shi.

Ya kara da cewa wajibi ne gwamnatocin jihohin Kaduna da Neja da Kebbi su yi aiki tare domin magance matsalar.

A ranar Lahadi ne dai Shugaba Buhari ya umarci sojoji da su yi amfani da karfi wajen yin maganin kashe-kashe da kuma garkuwa da mutane da ake fama da su a Jihar Neja.

Ko a ranar Laraba sai a aka samu rahoton kashe karin wasu mutum biyar a jihar ta Neja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button