Yadda Aka Cafke ’Yan Bindiga 10 A Dajin Kwara

Wasu ’yan bindiga 10 da suka addabi yankin Obbo/Aiyegunle zuwa yankin Ekiti na Jihar Kwara sun shiga hannu.

An cafke su ne bayan wani samame da jami’an tsaro suka kai tare da tarwatsa maboyarsu a cikin daji.

Yankin ya yi kaurin suna wajen sace mutane da yin garkuwa da su a baya-bayan nan, kuma an sha tsintar gawar mutanen da aka sace duk da biyan kudin fansa da ’yan uwansu ke yi.

Bayan damke su an samu muggan makamai da suka hadar da bindigogi, wukake, adduna da sauransu.

Babban Kwamandan ’yan bangar Jihar Kwara, Alhaji Saka Ibrahim, ya tabbatar wa Aminiya cafke ’yan bindigar.

A cewarsa, “An cafke mutum bakwai daga cikinsu a ranar Talata, sauran ukun kuma aka sake cafke a safiyar Laraba. Amma mutanenmu na ci gaba da shara a dajin.

“Za mu mika su ga ’yan sanda da zarar mun kammala bincike a dajin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button