Ya Hada Kai Da Abokansa Wajen Guntule Kan Budurwarsa Don Yin Tsafi

An shiga yanayin fargaba a yankin Oke Aregba da ke birnin Abeokuta na Jihar Ogun lokacin da aka kama wasu matasa suna babbake kan wata budurwar daya daga cikinsu, don yin tsafi.

Rahotanni sun ce ana zargin matasan sun guntule kan budurwar ne da nufin yin tsafin neman kudi.

Wakilinmu ya gano cewa wani mai gadi a unguwar mai suna Segun Adewusi ne ya gano matasan da sanyin safiyar Asabar, bayan ya lura da yadda suke dafa wani abu da bai yarda da shi ba a wata tukunyar kasa.

A nan ne bai yi wata-wata ba ya sanar da jami’an ’yan sanda da ke Adatan, inda suka je wajen suka kama uku daga cikinsu, yayin da daya ya cika wandonsa da iska kafin su isa wajen.

Wata majiya da ta tabbatar wa wakilinmu faruwar lamarin ta ce budurwar da aka hallaka din mai suna Rofiat, tana zaune ne a yankin Idi-Ape.

Majiyar ta ce Rofiat budurwa ce ga wani mai suna Soliu, wanda yanzu haka yake komar ’yan sanda.

Bayanai na nuna cewa Soliu ya yaudari budurwar tasa ne zuwa dakinsa, inda ya kwantar da ita ta karfin tsiya, sannan ya umarci abokansa su yanka masa ita.

A cewar majiyar, “Wadanda aka kama din sun hada da wani mai suna Wariz Oladeinde da Abdulgafar Lukman da Mustaqeem Balogun, dukkansu mazauna birnin na Abeokuta.

“Sun kashe Rofiat, sun gutsure kanta, suka saka gangar jikinta a buhu sannan suka fara dafa kan nata a tukunya. Sun shaida wa ’yan sanda a taron jama’a cewa tsafi suke kokarin yi da ita.

“Tuni ’yan sanda suka tafi da kan nata zuwa sashen adana gawarwaki na asibiti,” kamar yadda majiyar ta tabbatar wa wakilin namu.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce tuni suka kame uku daga cikin wadanda ake zargin.

“Bayan da muka titsiye su, sun kai jami’anmu wani kango inda suka jefar da gawar tata, kuma an kai ta asibiti domin gudanar da bincike. Mun kuma kwace wata karamar adda da wukar da suka yi amfani da su wajen kisan nata,” inji Kakakin ’yan sandan.

Source: Aminiya Dailytrust

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button