Wata Masifa Ta Ɓullo Kannywood Ana Zinah Da Mata Kafin A Sakasu Aciki Ta Hanyar ‘Yan Damfara

A Yan Kwanakinnane Wani Mummunan Al’amari Ya Fake Faruwa A Masana’antar Kannywood, Yadda Wasu Gurbatattun Mutane Suke Amfani Da Sunan Jarumai Suna Karban Kudi Awajen ‘Yam Mata Ko Kuma Suyi Lalata Dasu.
A Kwanakin Baya Babban Producer A Masana’antar Kannywood Abubakar Bashir Maishadda Ya Fitar Da Wata Sanarwa Akan Cewa Baya Amfani Da Kafar Sadarwa Ta Facebook Duba Da Matsalolin Da Ake Fuskanta A Shafin Daga Yan Damfara.
Sai Dai Baya Ga Producer Din Ya Wallafa Wannan Bidiyo Da ‘Yan Watanni Sai Kwatsam Asirin Daya Daga Cikin Masu Wannan Damfara Ya Tonu, Yadda Yake Karban Kudi Daga Wajen Mata Ko Kuma Yayi Lalata Da Wasu Da Sunan Abubakar Bashir Maishadda Akan Zai Sakasu Acikin Film.
Acikin Wata Bidiyo Da Abubakar Bashir Maishadda Ya Wallafa A Shafinnasa Na Instagram, Munga Wani Saurayi Yana Bayyana Cewa Shine Yake Yaudarar Wadannan ‘Yam Matan Akan Cewa shine Abubakar Bashir Mai Shadda Kuma Yana Karban Kudi Awajen ‘Yam Mata Ko kuma Yayi Lalata Dasu.
Ga Cikakken Bidiyon Sai Ku Kalla Anan: