Wani Ya Harbe Jaririyarsa Saboda Ba Ya Son Fara Haihuwar Mace

’Yan sanda a Pakistan sun bazama wajen neman wani mutum ruwa a jallo da ake zargi ya kashe ‘yarsa ‘yar kimanin kwanaki bakwai da haihuwa.

Ana zargin mutumin da harbe jaririyar ne saboda ba ya son ya fara haihuwar ‘ya mace sai dai namiji.

BBC ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne a birnin Mianwali da ke tsakiyar Pakistan.

Bincike ya nuna cewa jaririyar ta mutu ne nan-take bayan harbinta sau biyar da bindiga.

Kisan ya fusata jama’a tun bayan da aka sanya hoton gawar jaririyar a shafukan sada zumunta.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam a kasar sun ce kisan yarinyar da suka sanyawa suna Jannat na daga cikin kisan da aka yi wa kanana yara abin da kuma ba za su amince da shi ba har sai an bi mata hakkinta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button