Uncategorized
Da Dumi-Dumi: Jiga-Jigan APC sun bukaci Kotu ta dakatar da gangamin taron APC na ƙasa

Abuja – Fusatattun mambobin jam’iyyar APC sun bukaci babbar kotun tarayya dake Abuja, ta dakatar da kwamitin rikon kwarya na Mala Buni daga gudanar da babban taro na ƙasa a watan Fabrairu.
Mambobin da suka shigar da ƙarar sune, Suleiman Usman, daga Abuja, Muhammed Shehu, daga Zamfara da kuma Audu Emmanuel, daga Zamfara, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
A ƙara mai lamba FHC/ABJ/CS/3/2022, da lauyansu, Olusola Ojo, ya shigar, mambobin sun ce jam’iyyar APC na shirin saɓa wa dokokin ta idan aka bari ta gudanar da taron a Fabariru.
Cikakken bayani na nan tafe…
Source: Legit Hausa