Sojoji Sun Kashe ’Yan Boko Haram Sama Da 40 A Borno

Sojojin Najeriya karkashin rundunar tsaro ta Operation Hadin Kai sun karkashe ’yan Boko Haram da dama tare da kwace nakamansu a lokacin da suka yi kokarin kai har wani gari da ke Kudancin Jihar Borno.

Rundunar tsaron hadin gwiwa ta CJTF ta tabbatar da cewa yawan ’yan ta’addan da aka kashe a ba-ta-kashin na ranar Litinin ya haura 40.

Rahotanni sun ce ’yan ta’addan sun kwashi kashinsu a hannu ne a tsakanin garuruwan Maina da Hari, wadanda ke kusa da garin Biu na Jihar.

Wasu majiyoyi daga rundunar tsaro ta CJTF ta ce maharan sun zo ne cikin wasu motocin silke guda shida wajen misalin karfe 4:05 na yamma, amma kadan daga cikinsu ne suka samu tserewa da mota daya.

Majiyar ta ce, “Mun samu nasarar fatattakarsu tare da tarwatsa su cikin minti 45.

“Wannan ne aiki mafi kyau da muka yi a ’yan kwanakin nan, mun kashe ’yan Boko Haram sama da 40 a yau,” inji Haruna Aliyu, wani jami’in tsaro a rundunar ta CJTF.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button