Sanata Shehu Sani ya bukaci a hukunta wacce ta yi zina da kare

Wani labari wanda ya baza kafafen sada zumuntar zamani a ‘yan kwanakin nan shi ne yadda mata su ku wulakanta kan su a Dubai, Tashar Tsakar Gida.

Akwai wata sabuwar sana’a da su ke kira Potta Potty wacce ta ke yi wa karuwanci kaskanci, domin kuwa larabawa ne su ke yin wasu abubuwan kazanta da matan.

Cikin abubuwan kazantar sun hada da yi musu bahaya ko fitsaro a baki, wasu kuwa har da hada su da kare ko kuma wata dabba ta yi lalata da su a gabansu su na kallo su na dauka a waya.

Labarin wannan sana’ar ya dan kwana biyu ya na yawo a kafafen sada zumunta musamman na ‘yan kudu ana mamakin wannan sabuwar fitina ta karshen duniya.

Kwatsam sai ga wani bidiyo ya bayyana wanda ya nuna wata ‘yar Najeriya kare ya na amfani da ita wanda aka bayyana cewa wannan sana’ar ta iso Najeriya kuma 1.5m aka ba ta ta yi wannan bidiyon.

Yayin da ake tsaka da ta’ajjibi tare da mamakin wannan lamarin ne kawai sai ga wata budurwa ta bayyana a TikTok tana cewa ita ce ta yi bidiyo kare ya na saduwa da ita kuma babu komai don kare ya yi amfani da ita an ba ta 1.5m.

Kamar yadda ta ce, ba wata cuta ce ta kama ta ba, kuma saduwa kadai ta yi da kare ba kashe rai ta yi ba a dena yi mata surutai don yanzu haka morar kudinta ta ke yi.

Daga nan aka yi caa akanta yayin da aka dinga wallafa bidiyon ana ganin irin wannan tsaurin idon nata sannan aka dinga kira ga hukuma ta dauki mataki akanta.

Daga bisani budurwar ta kara dawowa shafinta na TikTok tana bayyana danasaninta tare da cewa ba ita tace ayi bidiyon ba, kawai ta yi hakan ne don nishadi da jan hankalin jama’a.

Ta ce har saurayinta ya rabu da ita sakamakon wannan bidiyon inda ta ce ta fuskanci tashin hankali mai tarin yawa.

Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ma ya magantu akan bidiyon inda ya bukaci a hukunta ta.

A cewarsa, hatta kwanciya kamar yadda kare ya ke yi bai dace ba balle lalata da kare.

Wannan bayani na Shehu Sani ya dauki hankali kwarai wanda daga bisani kuma ya goge bayanin daga shafinsa

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button