News

‘Babu Bangaren Da Buhari Ya Dauka A Rikicin Siyasar Kano’

Fadar Shugaban Kasa ta mayar da martani kan jawabin da bangare daya na Jam’iyyar APC a Jihar Kano ya yi cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da bangarensa.

Kakakin Shugaban Kasa, Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka a wata sanarwa da fitar mai taken ‘Shugaba Buhari yana goyon bayan Jam’iyyar APC, ba bangare daya ba’.

A sanarwar, Malam Garba ya musanta batun cewa Shugaban yana goyon bayan bangare daya a cikin bangarorin jam’iyyar da suke rikici a Jihar Kano.

A cewarsa, “Wannan ba zai yiwu ba alhalin lamarin na gaban kotu.

“Bisa tabbaci, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba ya goyon bayan kowane bangare.

“Goyon bayansa na Jam’iyyar APC ce dulkulalliya mai karfi, ba bangaranci ba.”

Wata Kotun Abuja ce a ranar 30 ga Nuwamba ta yanke hukuncin cire shugabancin jam’iyyar na bangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, inda ta ya ce tsagin bangaren tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ne zababbun shugabannin APC na hakika.

A tsagin Malam Ibragim Shekarau, Alhaji Haruna Danzago ne shugaba, a bangaren Gwamna Abdullahi Ganduje, Alhaji Abdullahi Abbas ne shugaba.

Shugaba Buhari ya gana da Gwamna Abdullahi Ganduje, sannan ya gana da Haruna Danzago.

Aminiya ta ruwaito Gwamna Abdullahi Ganduje yana cewa rikicin ba zai dauke masa hankali daga ayyukan ci gaban jihar da ya sa a gaba ba.

A cewarsa, “Yana da matukar muhimmanci kowa ya fahimci cewa hazakarmu da gogewarmu a siyasa ba za su bari wani karamin rikicin jam’iyya ya karkatar da hankalinmu wajen raya jiharmu ta Kano ba.

Abin da yake faruwa a yanzu ba wani abu ba ne face wani bangare na siyasa da ya zama al’ada a tsarin dimokuradiyya.”

An yi ta kai ruwa rana a tsakanin bangarorin biyu bayan hukuncin kotun, sai dai akwai Kotun Daukaka Kara da Kotun Koli da za a iya zuwa kafin a kammala shari’ar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button