N-Power Batch C2 Zasuyi Thumbprint Domin Karƃar Payment 2022

Hukumar  N-Power ta sanar da dukkan wadanda suka cike tsarin na N-Power kuma suka samu wato Batch C2 da su hanzarta domin yin Thumbprint wanda hakan shine zai bada damar kammala rijistar.

Wannan sanarwa ta fito ne daga shafin sada zumunta na hukumar inda takara da cewa dukkan Applicants zasu shiga dashboard dinsu ne inda a nan ne zasuyi wannan tantancewa  ta yatsun hannu.

Bugu da ƙari hukumar tace za’a iya zuwa café mafi kusa domin  yin wannan Thumbprint akan lokaci duba da yadda mutane da dama ne ke bukatar yi a dukan fadin kasa.

Hukumar ta kara cewa dukkan wanda ya kammala Verification na Thumbprint print sai ya zama yana ziyartar dashboard dinsa domin ta nan ne za iya ganin inda za dora ko kuma wani sabon bayani.

Bayan dashboard din kuma shima email yana daya daga cikin hanyar sanar da Applicants halin da ake ciki ko kuma idan da wan I update to zai sami sanarwar ta Email dinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button