Mutum Miliyan 13 Na Fuskantar Barazanar Yunwa A Afirka – MDD

Hukumar Kula da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP), ta yi gargadin cewa akwai kimanin mutum miliyan 13 da ke fuskantar barazanar tsananin yunwa saboda farin da aka fuskanta a sassa da dama na nahiyar Afirka.

Hukumar dai ta ce farin da aka fuskanta sakamakon karancin ruwan sama da aka fuskanta a shekara uku a jere na matukar barzana ga nahiyar.

A cikin wata sanarwa da Daraktan hukumar da ke Gabashin Afirka, Michael Dunford ya fitar ranar Talata, hukumar  ta ce, “Karancin ruwan ya kawo cikas a bangarori da dama, dabbobi na mutuwa, yunwa na karuwa sannan fari na dada kunno kai.

“Lamarin na bukatar a kawo daukin gaggawa da kuma kai tallafi a kai a kai don taimaka wa iyalai da dama.”

Daukewar ruwan sama kafin lokacin da aka saba gani a kasashen Afirka da dama dai da kuma tashin farashin gwauron zabin da kayan abinci da na sauran masarufi ke yi da kuma raguwar bukatar mutane su yi aiki a gonaki ya dada ta’azzara matsalar.

WPF dai ta ce barazanar na tilasta wa iyalai da dama yin kaura zuwa wasu yankunan, inda ta yi barazanar karuwar rikice-rikice in ba a kai wa mutane dauki ba.

Hukumar dai ta sha yin gargadi kan barazanar farin da kuma yiwuwar uskantar matsalar yunwa, wadanda za su iya rura wutar rikici a yankunan nahiyar da ma wasu sassa na nahiyar Asia.

Source: Aminiya Dailytrust

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button