Mutum 5 Sun Mutu A Wajen Hakan Yashi A Kano

Akalla mutum biyar ne aka tabbatar sun mutu bayan da wajen da suke hakar yashi ya rufta tare da danne su a kauyen ’Yanlami da ke Karamar Hukumar Bichi a Jihar Kano.

A cewar wata sanarwar da mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Abdullahi, wanda ya tabbatar da hakan, ya ce lamarin ya faru da safiyar ranar Asabar.

Ya ce, “Mun samu kiran gaggawa daga ofishin shiyyarmu na Bichi cewa tarin yashi ya danne mutum biyar. Mun aike da jami’anmu zuwa wajen da misalin 11:05 na safe,” inji Saminu a cikin sanarwar.

Ya ce mutanen da lamarin ya shafa sun hada da Alasan Abdulhamid masi shekara 22 da Jafaru Abdulwahabu mai shekara 30 da Jibrin Musa mai shekara 30 da Masa’udu Nasiru mai shekara 25 sai kuma Muhammad Sulaiman mai shekara 35.

Kakakin ya ce yashin ya danne matasan ne lokacin da suke kokarin tono shi da nufin taya wani abokinsu da ke shirin yin aure.

Hukumar dai ta ce tuni aka tono gawarwakin mutanen sannan aka mika su ga ’yan sanda da kuma Dagacin ’Yanlami don yi musu jana’iza.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button