Moppan tayi kira ga ‘yan kannywood da su daina yiwa junan su tone-tonen asiri kan al’amarin da ya faru

Kungiyar masu shirya fina-finai ta Arewacin Nageriya wato “Moppan” ta kargadi ‘yan masana’antar kannywood da su daina yiwa junan su tone-tonen asiri, musamman ma a shafukan sada zumunta sakamakon maganar da Naziru Sarkin waka ya fada wanda har ta janyo cece-kuce a kwanan nan.

A wata sanarwa da kungiyar “Moppan” ta fitar wacce ta samu mai dauke da sa hannun mai magana da yawunta Al-Amin Ciroma, tace ta yanke shawarar jan kunnen ‘yan kungiyar kannywood ne a yayin da ake cigaba da tafka tsattsamar mahawara dangane da rigingimun da suka biyo bayan tattaunawar da gidan jaridar BBC Hausa tayi da Hajiya Ladin Cima.

Ta kara da cewa, Mun lura lamarin yana dauke da wani salo na daban har ila yau, zancen na cigaba da jan hankalin al’umma musamman mabiya al’amuran fina-finan Hausa, inda kowa ke tofa albarkacin bakinsa dangane da zancen.

Kamar yadda sanarwar ta kara fadin cewa, Hakan ta sa wasu masu ruwa da tsaki suka fara kiraye-kiraye ga shugabannin “Moppan, da su shiga su magance muhawarar da ‘yan kungiyar kannywood din suke tafkawa.

MOPPAN ta ƙara da cewa mutane da ƙungiyoyi da dama sun aika mata buɗaɗɗun wasiƙu kan cewa ta tsawatar kan lamarin.

Shugaban “Moppan” din Dr, Ahmad Muhammad Sarari yace, sanin muhimmancin kiraye-kirayen ne ya sa kungiyar ke tabbatar wa al’umma cewar ta dauki kwararan matakai, da hadin gwiwar sauran kungiyoyi kamar kungiyar masu shirin fim ta Arewa wato “AFMAN” dangane da lamarin.

Baya sanarwar BBC ta sake tuntubar mai magana da yawun “Moppan” Al-Amin Ciroma wanda yace, lamarin na ‘yan Kannyowwod na neman wuce gona da iri.

Abu ya faru kan hirar da aka yi da Ladin Cima amma sai jan magana suke ta yi har hakan ta sa an shiga wata gabar ta zarge-zarge da jifa juna da kalamai marasa dadi.

A cewar sa, mafi ban takaici shi ne yadda suka bazama shafukan sada zumunta irin su Tiktok da Instagram da Facebook, wurare marasa sirri suna takalar juna.

Al-Amin Ciroma ya ci gaba da cewa, dole ne “Moppan” ta taka musu burki sabida abin nasu ya koma kai wa juna hari da jifan juna da gore-gore da zarge-zarge da kalaman batanci.

Kungiyar “Moppan” dai ta bayyana cewa, ta dauki wasu matakai kan wannan lamari daga cikinsu akwai jawo hankalin dukkanin bangarori da su dakata da musayar yawu.

Haka kuma “Moppan” din zata cimma matsaya ta musamman kan lamarin, bayan shirye-shirye da dama da ta gudanar.

A karshe dai shugabannin kungiyoyin na “Moppan” suna kara kira ga dukkanin ‘yan Kannywood da su kasance masu kishin masana’antar, kuma su daina bin son zuciya da zai iya kawo manyan matsaloli ga sana’ar fim baki daya.

Sannan kuma “Moppan” tana kira da a yada wannan magana a kowace kafar yada labarai da sadarwa.

Bayan haka kuma “Moppan” zata cimma matsaya bayan kammala tattaunawa da sauran kungiyoyi da masu ruwa da tsaki a harkar da kuma dattijai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button