Mawakiyar Tiwa savage dake kudancin Nageriya ta bayyana rashin jin dadin ta dalilin Aliko Dangote bai zama Mahaifin ta ba

Ficacciyar mawakiyar nana ta kudancin Nageriya Tiwa savge ta bayyana cewa, taso ace Aliko Dangote shi ne mahaitin ta sabida yafi kowa kudi a Afrika.

Tiwa savage ta bayyana hakan ne a shafin na Snapchat a ranar alhamis data gabata, inda ta bayyana bakin cikin ta akan yadda ta sha wahala wajan yin kudi, kamar yadda Dimokuradiyya ra tuwaito.

Mawakiyar Tiwa Savage ta yi rubutu kamar haka: Ina da wani taro amma ba abu ne mai sauki wajan yin kudi ba Allah ne ya taimake ni, amma mai yasa Baba na bai zama Dangote ko kuma wani kamar haka ba.

Mahaifin Tiwa savage ta rasu ne a ramar sha tara 19 ga watan Yuli shekarar 2021, inda aka aka binne shi a Jihar Lago, amma sai tace bayan rasuwar mahaifin nata ne ta fara shan kwaki da ruwa.

A lokacin da Tiwa savage takw bayyana yadda rasuwar mahaifin nata ta kasan ce a kafar sadarwa, ta bayyana shi a matsayin mutum mai karfafa mutane.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button