Matashi Ya Yi Wa Matar Aure Duka A Gidanta Ya Lahanta Mata Ido

An gurfanar da wani matashi a gaban Kotun Shari’ar Musulunci da ke Unguwar PRP Kano bisa zargin sa da lahanta idon wata matar aure.

Tun da farko ’yan sandan farin kaya ne ne suka gurfanar da mutumin bisa tuhumar sa da cewa ya shiga gidan wani mutum, inda kuma ya sami matar magidancin ya yi mata dukan kawo wuka har ya lahanta mata ido.

Sai dai wanda ake zargi ya amsa laifukan da ake zargin sa da shi da suka hada da shiga gida da yi wa matar mummunan rauni.

Ya kuma shaida wa kotun cewa ya daki matar ce saboda damun sa da take da kiran masu magana, wanda kuma hakan ya ce yana kuntata wa mahaifiyarsa.

Alkalin kotun, Isa Rabiu Kademi Gaya, ya bayar da umarnin tsare wanda ake zargi a gidan yari zuwa ranar 11 ga watan Fabrairu mai zuwa don ci gaba da sauraren shari’ar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button