Kungiyar matan kannywood zasuyi karar Naziru Sarkin waka idan bai janye kalaman daya fada akan su ba

Sakin layin da Naziru M Ahmad ya yi wanda aka fi sani da Sarkin waka akan ‘yan kannywood kan maganar lalata da ‘yam mata kafin a sanya su a shirin fim, wannan maganar ta janyo masa cece-kuce da maganganu kala-kala.

Bayan jarumai da Daraktotin masana’antar sun sha tofa albarkacin bakin su kan maganar da Sarkin waka ya fada akan su, to a yanzu kuma jarumai mata na masana’antar kannywood sun yi gangami domin daukar mataki akan maganar da Sarkin waka ya fada akan su.

A yau ne wani rahoton takarda ya fito daga shugabancin Hauwa A Bello kan maganar da Naziru Sarkin waka ya fada a kan su na sai anyi lalata da su ake sanya su a shirin fim.

Wanda maganganun da Sarkin waka ya fada sun tada kura a masana’antar kannywood bayan Ladin Cima tayi shira da BBC Hausa, har ta bayyana musu kudin da ake bata a harkar tasu ta fim inda tace ma ba’a taba bata sama da dubu biyu ko uku ko biyar ba.

To a yau kuma shine kungiyar matan kannywood Association suka fitar da wata takarda zuwa ga Naziru M Ahmad wato Sarkin waka, inda takardar take cewa.

Assalamu alaikum,
Kungiyar matan ‘yan kannywood women association of nigeria (k-wen) karkashin jagorancin shugabancin ni shugabar kungiyar a madadin yan kungiya.

Duba da abin da ya faru wanda naziru M Ahmad yayi wasu kalamai na chin zarafi ga mata masu sana’ar fim muna kira a gare shi da ya janje kalamansa cikin kwana ukku da yau in kuwa bai yi haka ba zamu kaishi kotun musulunci bisa tuhumar yayi mana kazafi.

Nagode.

Hauwa A Bello.

Shugaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button