Kotun Koli Ta Tabbatar Wa Tsagin Ganduje Shugabancin APC Na Kano

Kotun Koli ta tabbatar wa da tsagin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano shugabancin jam’iyyar APC na jihar.

Wannan na zuwa ne bayan daukaka kara da tsagin tsohon Gwamnan Jihar, Ibrahim Shekarau ya yi na neman ta ayyana Haruna Danzago a matsayin shugaban jam’iyyar APC na jihar.

Kwamitin Alkalai na kotun mai mambobi guda biyar, karkashin jagorancin Alkali Inyang Okoro ne ya yanke hukuncin a ranar Juma’a.

A cewar Mai shari’a Okoro, Kotun Daukaka Karar da ta saurari karar da gabarta mata da farko ba ta da hurumin yin haka, don haka karar ta zama abar korewa.

Haka nan, Kotun Kolin ta ce hukuncin da ta yanke ya shafi sauran kararraki biyun da aka daukaka a shari’ar.

Karin bayani na nan tafe……

Source: Aminiya Dailytrust

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button