Karamar Sallah: Bana Iya Bacci Saboda Halin Da ‘Yan Nijeriya Ke Ciki Kan Sha’anin Tsaro – Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya bayyana cewar, matsalar tsaro da ke addabar wasu sassan Nijeriya na hanashi barci, inda ya ce bai samun isashshen barci kan wannan kalubalen.
Buhari ya bayyana hakan ne lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai bayan idar da Sallar Idin a Abuja, ya nuna cewa zai cigaba da bada himma da kwazo wajen ganin an samu nasarar shawo kan matsalolin tsaron.
Sannan, ya sha alwashin cewa ba za su taba yin kasa a gwiwa ba har sai sun kawar da ‘yan ta’adda tare da dakile duk motsinsu domin tsarkake kasar daga miyagun ‘yan ta’addan.
- Gwamnati Za Ta Fara Daure Iyayen Mabarata A Edo
- Goodluck Jonathan Ya Yi Wa Al’umar Musulmin Najeriya Barka Da Sallah
Kamfanin Dillacin Labarai na kasa (NAN) ya labarto cewa Buhari da iyalansa da hadimansa da jami’an gwamnati da sauran jiga-jigan kasa sun halarci filin sallar Idi na Mambila Barak, Abuja wajejen karfe 9 na safiya.
Babban limamin Barak, Muhammad Dahey-Shuwa, shi ne ya jagoranci sallar Idin, inda ya tunatar da musulmai muhimmanci gudanar da abubuwan da suka koya a watan Ramadana.
Source: Leadership Hausa