Kannywood

Rarara Ya Gwangwaje ’Yan Kannywood 57 Da Kyautar 50,000 Kowannensu

Fitaccen mawakin wakokin siyasar Kannywood, Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara ya gwangwaje ’yan Kannywood mutum 57 da kyautar kudi N50,000 kowannensu.

Hadimin mawakin kan kafafen watsa labarai, Rabiu Garba Gaya ne ya bayyana haka, inda ya ce tallafin na ciki ire-iren ayyukan kungiyar 13×13, wadda Rarara ke jagoranta.

A cikin sanarwa da ya sanya wa hannu, ya ce an bai wa jarumai iyaye mata 13 da jarumai iyaye maza 15 kyautar 50,000 kowannensu.

Sannan ya ce Rarara ya bai wa jarumai mata 10 kowanensu kyautar 50,000, yayin da kuma mawaka mata masu aure suka samu kyautar 30,000 kowannensu.

Tuni wadanda suka ci gajiyar tallafin suka shiga bayyana godiyarsu ga mawakin a shafukansu na sada zumunta.

Sabuwar tafiyar 13×13 wadda Rarara ke jagoranta ta kunshi jarumai, mawaka, furodusoshi da daraktoci daga masana’antar shirya fina-finan Kannywood a matsayin ’ya’yan kungiyar.

Idan ba a manta ba a baya-bayan nan mambobin 13×13 suka dawo daga birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) inda suka je yawon shakatawa da kungiyar ta dauki nauyi.

Source: Aminiya Dailytrust

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button