Kannywood

Makiya da mahassada na basa farin ciki dani sabida na shiga shirin fim na kasar India, cewar jaruma Rahama sadau

Makiya da mahassada na basa farin ciki dani sabida na shiga shirin fim na kasar India, cewar jaruma Rahama sadau

Shahararriyar jaruma kuma ficacciya mai tashe a shirin fina-finan Arewacin Nageriya da Kudancin ta Rahama sadau wanda a yanzu haka tana taka mushimmiyar rawa a cikin shirin wani fim na kasar India mai sun, Khuda Haafiz.

Jaruma Rahama dasau ta nuna godiyarta ga Allah bisa damar da ta dade tana nema na samin shiga cikin fina-finan da suka sharaha, da kuma fitattun wakoki da tallace tallace na cikin kasar Nageriya har ma da wajen ta.

A cikin wani sako da jaruma Rahama sadau ta wallafa a shafin na kafar sada zumunta ta fadi cewa: Duk da cewa an dakatar dani ko kuma an kore ni daga kannywood, duk lokacin dana shiga wata matsala Allah yana sa kana ya zama alkairi a gare ni.

Wannan dalilin ne yasa jaruma Rahama sadau ta mafa wata kungiya mai zaman kanta mai suna, Today’s Care, don kula da mabukata da kuma godiya ga Allah da ya daga daukakarta, ya kuma kare ta daga abokan gaba sannan da wadanda basa mata fatan alkairi ko san ganin cigaban ta a harkar wasan kwaikwayo kamar, Hausadailytime ta ruwaito.

Jatuma Rahama sadau ta kara da cewa: Tuni na zama shahararriyar tauraruwa ta kasa da kasa kuma ‘yar kasuwa dake cikin rufin asiri, don haka wannan baya nufin bazan koma masana’antar kannywood naci gaba da wasan kwaikwayo ba.

Ta kara da cewa: Zan koma cikin babban shiri kuma na zama babbar furodusa, inda tunanin bude gidan cinema a Kaduna domin mutane surika zuwa hutawa tare da iyayan su a lokacin bukukuwa.

Rahama sadau tace: A duk lokacin dana yanke shawarar na shiga wasu ayyuka abin da nake tunani shine mahaliccina ba masu zagina cikin ayyukana ba, iyayena suna raye gani da ‘yan uwana sannan ako da yashe suna yimin addu’a domin Allah ya kiyaye ni daga abokan gaba kuna gaskiya ne, addu’ar da iyayena da ‘yan uwana suke min ta zama katanga mai karfi a tsakanina da makiyana.

Ta kara da cewa: Ako da yaushe ina samin nasara akan aikin dana zaba nayin wasan kwaikwayo a yanzu haka ina kasar Indina muna daukar wani sabon fim wanda ina a matsayin babbar jaruma kuma mai jagorantar sabon shirin, sannan ina jin yaren india sosai wanda karin wata dama ce a gare ni a lokacin da nake birnin New York tare da wasu fitattun mawaka, na riga na shiga Nollywood yanzu sunan Rahama sadau ya shiga kundin, Halla of Fame, inda manyan mutane maza da mata ne kawai zasu iya shiga wannan kundin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button