Kannywood

Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un: kalli yadda aka gudanar da Jana’izar rasuwar Jarumin Kannywood Malam Lawan

Kamar yadda kuka sani Masana’antar shirya Fina-Finan Hausa ta Kannywood tana da Jarumai Maza da Mata da yawa wanda ba kowa ne ya san wasu daga ciki ba.

Related Articles

Inda har ma wani lokacin sai a yi rasuwa wasu basu san wanene ya rasu a cikin Jaruman Masana’antar ba duba da yadda suke da yawa sosai, inda wasu ma sun yi shekaru da yawa a cikin Masana’antar basu yi sanuwar da ana fadar su za’a gane su ba.

To a yau ne muka wani gar da labarin rasuwar wani daga cikin Jaruman na Kannywood wanda Jama’a da dama basu sani sosai ba, amma dai ana dan yawan ganin sa a cikin shirin Fina-Finan Hausa a wasu lokutan.

Malam Lawan

Mun sami labarin ne daga dan uwansa abokin sana’arsa Abba Elmustapha inda ya wallafa a shafin sa na sada zumunta cewa: Allah yayiwa Jarumin Rasuwa inda ya wallafa a shafin sa kamar haka.

INNALILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UNAllah yayiwa Jarumin barkwanci MALAM LAWAN Rasuwa kuma anyi janaizarsa kamar yadda Addinin Musulunci ya tanadar.

Mun Addu’a Allah ya jikansa ya gafarta masa kurakuransa yasa Aljanna ce makomarsa, Idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da imani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button