Kannywood Ta Dauki Zafi Kan Maganar Biyan Hakkin ’Yan Wasa

Advertisement

Jiga-jigan masana’antar fim ta Kannywood sun fara nuna wa juna yatsa bayan dattijuwa kuma jarumar masana’antar, Ladin Chima, ta shaida wa sashen Hausa na BBC cewa an biya ta N2,000 kudin fitowa a fim.

Mawaki Naziru M. Ahmad, wanda aka fi sani da Sarkin Waka, ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na Instagram, inda kalubalanci jarumi Ali Nuhu da darakta Falalu Dorayi a kan musanta batun biyan Ladin Chima N2,000 da ta ce an yi a matsayin kudin fitowa a fim.

“… Gaskiyar magana ’yan fim ba Allah a ransu, duk wanda suka yi magana a kan matar nan babu Allah a ransu kwata-kwata.

“Yanzu saboda Allah Ali Nuhu da Falalu Dorayi za su ce ba su san ana daukar N2,000 ko N1,000 ana ba wa tsofaffin nan ba idan sun tashi daga fim ba?

““Ku ji tsoron Allah mana, kowa ya san masana’antar nan (Kannywood) tana fama da matsaloli daban-daban, wasu ma su suke biyan kudin a saka su a fim, wata ko ta bada kudi ko ki bada kanki.”

Mawakin ya ce lamarin ba boyayyen abu ba ne, duk wani da ke cikin masana’antar ya san abin da ke faruwa, inda ya bukaci a shafa wa dattijuwar lafiya don ta huta.

“Mun san wannan; Duk wanda zai fito sau daya ko biyu a fim irin wannan kudi ake dauka ana ba shi, ba shi ya sa harkar ta yin kasa ba, idan kuna da niyyar gyara ku fito ku gyara,” a cewar Sarkin Waka.

Mawakin ya shafe minti 6:45 a cikin bidiyon inda ya yi raddi kan maganar Ali Nuhu da Falalu Dorayi kan cewa sun taba daukar kudi N40,000 zuwa sama sun ba wa Ladin Chima.

Ladin Chima: An yi Ca a kan Sarkin Waka

Sai dai martanin sarkin waka bai yi wa wasu dadi ba a masana’antar fim din.

Furodusa Abubakar Bashir Maishadda, ya fito ya caccaki Naziru Sarkin Waka cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Instagram.

“…Maganar da Mama Tambaya ta yi a kan cewa ba a taba ba ta kudi sama da N2,000 ko N5,000 wannan ba haka ba ne, zan yi mata uzuri.

“Amma ita ma ta san mutane da yawa sun ba ta sama da wannan kudin a ciki har da ni (Abubakar Bashir Maishadda), akwai Ali Nuhu, akwai Falalu Dorayi da sauransu.

“Mu a Kannywood babu wanda ya taba mana aiki muka hana shi kudinsa, inda akwai wanda muka taba cinye wa kudi ya fito ya fada mana.

“Ka fito kana wasu soki-burutsu a kafafen sada zumunta, kai ba ka isa ka taba mana masana’anta ba mu mayar maka da martani ba, ba ka isa ba.

“Kai ya kamata a tambaya wanda suke fim ba a biyan su saboda mu ba mu san shi ba, don mu ba ma yi a ayyukanmu ba ma yi.

“…Saboda haka idan kana soki-burutsunka, ka san me ka ke fada, saboda mun fahimci kana son taba mutuncin masana’antar nan da martabar masana’antarmu, wannan masana’antar ba mu da abin da ya fi ta.

“Don haka wallahi Naziru ba ka isa ba, duk lokacin da ka fito ka yi magana sai mun ba ka amsa; Yauwa, ka kiyaye! Babu wanda yake jin tsoron ka a cikinmu kuma babu wanda ka isa ka fito ka yi wa magana a nan bai ba ka martani ba, saboda haka ka kiyaye wallahi,” inji Maishadda.

Shi kuma forudusa Alhaji Shehe, a mataranin da ya yi wa Sarkin Waka, ta Instagram ya ce wa mawakin ya ji tsoron Allah.

“Maganarka Naziru akwai kura-kurai da yawa, ka ji tsoron Allah. Sannan ka daina fadar maganar da ba ka da cikakkiyar masaniya a kai.”

Kafin wannan martanin da ya yi wa Naziru, forodusan shi ma ya yi martani ga Ladin Chima, inda ya ce daga cikin alamomin munafiki akwai fadin karya.

Sannan ya kara da cewa mutum mai shekaru irin nata ya zauna hira da ’yan jarida ya fadi abin da ba haka ba, to lallai ya kamata a tausaya mata.

Tuni dai lamarin ya dauki hankalin mutane da dama daga cikin har da wajen masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood, inda kowa ke tofa albarkacin bakinsa kan lamarin.

Mama tambaya ta tayar da kura a Kannywood

Ladin Cima ta tayar da kura a masana’atar ne bayan ta bayyana a wata tattaunawarta da BBC cewa ba a taba biyan ta N50,000 ko 30,000 ko 20,000 ba a fim.

A cikin hirar da shirin na ‘Daga Bakin Mai Ita’ ya yi da ita, ta bayyana cewa fim na karshe da ta je ma dubu 2 aka biya ta.

Fitar hirar tata ke da wuya wasu daga cikin masu-fada-a-ji a masana’antar suka fito suna yi mata raddi.

Daga cikin masu yi mata raddi akwai marubuci a masana’antar, Nazir Adam Salihi, wanda ya karyata dattijuwar, inda ya shi da kansa ya taba biyan ta kudade masu kauri.

Nazir wallafa a shafinsa na Facebook cewa, “Na biya Ladi Cima (Tambaya) N4o,000 a fim din Gidan Badamasi Kashi na uku; na sake biyan ta N30,000 a kashi na hudu.

“Haka nan ko wata daya ba a yi ba na sake biyan ta N30,000 a wani dan bidiyo na fadakarwa kuma a duka ba ta yi fitowa sama da goma ba.

“Haka nan mun yi gyaran scene guda wanda magana kawai ta yi muka biya ta N5,000 muka kuma saya mata abinci na kusan N4,000 a wuni guda.

“Haka nan a gabana, Hadiza Gabon ta ba ta N270,000 kyauta! Amma duk da haka ka ji halin dan Adam. Kai jama’a!” inji shi kamar yadda ya rubuta a Facebook.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button