Jarabar mijina ta yi yawa, yana so ya kashe ni da saduwa, Matar aure ga kotu

  • Olamide Lawal, wata matar aure mai yara uku, ta garzaya kotu tana neman a datse igiyan aurenta da mijinta, Saheed Lawal
  • Olamide ta koka da cewa mijinta ba shi da aikin yi sai shan giya ya yi tatul, tare da dukanta da tilasta mata kwanciya da shi ba kakautawa
  • A bangarensa, mijin matar, Saheed Lawal ya roki kotun ta taya shi tattausa zuciyar matarsa yana mai cewa ya tuba kuma zai sauya halayensa

Ibadan – Wata matar aure mai ‘ya’ya uku, Olamide Lawal, a ranar Juma’a ta roki kotun Kwastamare da ke zamansa a Mapo, Ibadan, ya raba aure tsakaninta da mijinta, Saheed Lawal, saboda yana jarabar ta da yawan saduwa, rahoton Premium Times.

A karar da ta shigar, Olamide wacce ke zaune a Ibadan ta kuma yi ikirarin cewa mijinta ya saba shan giya ya yi tatil yana maye, The Nation ta ruwaito.

Matar aure
Jarabarsa ta yi yawa, a raba mu kafin ya kashe ni, Matar aure ta fada wa kotu. Hoto: The Nation Source: Twitter

Ta ce:

“Mun shafe shekaru 14 muna zaman aure da Lawal. Tantirin mashayin giya ne kuma ba shi da tausayi ko kadan a zuciyarsa.

“Abin da ya mayar da hankali a kai shine shan giya, duka na da kuma tilasta min kwanciyar aure da shi. Baya kulawa da yaran mu.

“Ba zan iya cigaba da zama tare da shi ba.”

Lawal ya roki kotu ta bashi dama ya yi sulhu da matarsa

A bangarensa, Lawal ya roki kotun ta taimaka ta bawa matarsa hakuri domin ta cigaba da zama da shi.

Lawal, wanda sana’ar dinki ya ke yi ya ce:

“Na yi nadamar abin da na aikata kuma a shirye na ke in sauya rayuwa ta. A shirye na ke in fara bawa matata da yara na kudin abinci.”

Alkaliyar kotun, Mrs S.M. Akintayo ta dage cigaba da sauraron karar har zuwa ranar 1 ga watan Maris domin yanke hukunci, ta kuma shawarci ma’auratan su tabbatar sun cigaba da zaman lafiya.

Source: Legit Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button