ISWAP Ta Kashe Mayakan Boko Haram 8 A Borno

Kungiyar ISWAP mai da’awar jihadi a Yammacin Afirka, ta kashe mayakan Boko Haram takwas a wata karawa da suka ka yi a Jihar Borno.

Zagazola Makama, wani Kwararren Manazarci kan Yaki da Tayar da Kayar Baya kuma mai fashin baki kan sha’anin tsaro a Yankin Tafkin Chadi, ya ce lamarin ya faru ne a garin Jilli da ke tsakanin Kananan Hukumomin Gubio da Magumeri na Jihar Borno.

Wakilinmu ya ruwaito wani jami’in leken asiri yana shaida wa Zagazola Makama cewa, ISWAP ta yi wa mayakan na Boko Haram kwanton bauna ne a yunkurinsu na sace dabbobin mutanen yankin da ke Arewacin Borno.

Kazalika, Zagazola ya ce baya ga kashe mayakan Boko Haram takwas da ISWAP ta yi, ta kuma samu nasarar kwace makamansu da babura.

A bayan nan dai ana zargin cewa yunwa ta addabi sansanonin kungiyar Boko Haram a yankin Bama a sakamakon karancin abinci.

Bayanai sun ce hakan ce ta sa mayakan ke kai hare-hare a kauyukan yankin da gonaki don samun kayan abinci, kudi, magunguna da sauransu.

Aminiya ta ruwaito cewa a ranar 3 ga watan Yuli, an gano gawarwakin manoma uku a Gajeri, wani kauye mai tazara kadan da Karamar Hukumar Konduga ta Jihar Borno, bayan wani hari da wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka kai musu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button