Hatsarin Mota Ya Yi Ajalin ’Yan Sanda Uku A Abuja

Advertisement

Akalla jami’an ’yan sanda uku ne suka riga mu gidan gaskiya a wani mummunan hatsarin mota da ya ritsa da su a kan babbar hanyar Kubwa zuwa Zuba daura da Rukunin Gidajen Gwarimpa da ke Abuja, babban birnin kasar. 

Aminiya ta ruwaito cewa, hatsarin ya auku ne yayin da kan motar rundunar ’yan sanda ta musamman ta kwace inda ta rika kundubala har ta kai ga fada wa wata babbar magudanar ruwa.

Wani ganau mai suna Musa da ya zanta da wakilinmu, ya shaida cewa hatsarin ya auku ne a yayin da daya daga cikin tayoyin motar ta fashe saboda tsabagen gudun da ake tsalawa.

Musa ya bayyana cewa, motar yan sanda nan take ta sauka daga kan titi inda ta fada wata magudanar ruwa inda a nan jami’an ’yan sandan uku suka mutu yayin da ragowar wadanda ke cikin motar suka jikkata.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Abuja DSP Josephine Adeh da wakilinmu ya tuntuba, ta tabbatar da faruwar lamari wanda ta bayyana a matsayin abun takaici.

“Wannan lamari abun takaici ne saboda mun rasa jami’anmu,” a cewar Adeh.

Source: Aminiya Dailytrust

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button