Gwamnatin Tarayya Ta Haramta Sayar Da Amfanin Gona Ga ’Yan Ketare

Gwamnatin Tarayya ta amince da bukatar haramta wa baki ’yan kasashen waje sayen amfanin gona kai tsaye daga manoma ko kuma amfani da wakilansu.

Wannan dai na zuwa ne a matsayin wani yunkuri na bunkasa harkokin kasuwanci a cikin gida.

Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Zuba jari, Otunba Adeniyi Adebayo ya bayyana matakin bayan taron Majalisar Zartarwa wanda Matamakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta a ranar Laraba.

Adebayo ya ce sakamakon amincewa da wannan shirin, ’yan kasuwar cikin gida ne kawai da ke da lasisin yin cinikin amfanin gonaki kai tsaye daga manoma domin sayarwa baki ’yan kasashen waje.

Ministan ya ce wannan mataki zai toshe kofar cutar manoman da bakin ke yi wajen karbe amfanin gonakin su da ’yan kudi da ba su taka kara sun karya ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button