Gwamnatin Kano Ta Sa A Tono Gawar Wani Almajiri

Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da umarnin tono gawar wani almajiri wanda ake zargin malaminsa da halaka shi.

Kwamishinan Harkokin Addinai a jihar Dokta Muhammad Tahar Adamu (Baba Impossible) ne ya bayyana haka yayin da yake bankado makarantar ’yan marin da ke unguwar Wailari a jihar.

Related Articles

Aminiya ta rawaito cewa ana zargin malamin da yi wa almajirin dukan kawo wuka, lamarin da ya yi ajalinsa.

Haka kuma rahotanni sun bayyana cewa lokacin da almajirin ya rasu ba a sanar da iyayensa ba aka je aka binne shi.

Baba Impossible ya bayyana cewa gwamnatin ta sa ’yan sanda su hako gawar almajirin tare da gudanar da bincike don gano musabbabin rasuwarsa.

“’Yan sanda za su yi nasu bincike bayan an gudanar da bincike likitoci a kan gawar don gano abin da ya yi ajalinsa,” inji shi.

Kwamishinan ya kara da cewa idan har aka sami malamin da laifin to za a gurfanar da shi gaban kuliya don girbar abin da ya shuka.

Shi ma da yake nasa jawabin, Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa a yanzu haka mai makarantar da sauran wadanda ke taimaka masa suna hannu.

“Akwai rahoto da muka samu cewa duk da dokar Gwamnatin Jihar Kano ta haramta makarantun ’yan mari amma akwai wasu mutane da ke ci gaba da gudanar da irin wadannan makarantu.

“Ga shi mun sami wani daki a kulle a wannan makaranta inda muka taras da yara cike a ciki. Hakan ya sa muka kama mai makarantar za kuma mu tafi da shi don amsa wasu tambayoyi.

“Yanzu haka mun fara gudanar da bincike domin gano gaskiyar lamarim,” inji Kiyawa.

Malam Musa Safiyanu, ya ce duk da cewa ana gudanar da makarantar amma shi ba ya azabtar da almajiransa.

“Ina sane cewa gwamnati ta hana makarantar ’yan mari amma ni ba a kan irin wannan tsarin nake gudanar da makarantata ba.”

Haka kuma malamin ya musanta zargin kisan almajirin inda ya bayyana cewa, “Idan an yi bincike za a ga cewa ba ni da hannu haka kuma ban yi sakaci wajen mutuwarsa ba.”

A yanzu haka dai wannan makaranta na garkame bayan an kubutar da matasa da yara da dama wadanda ake kokarin mayar da su ga iyayensu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button