Gwamnatin jihar Bauchi zata aurar da tubabbun Mata Karuwai a kalla guda 100 bayan an koya musu sana’o’i

Kamar yadda Muryoyi ta ruwaito cewa, a ranar Talata Gwamnatin Bauchi ta yi wani shiri na koyar da sana’o’in hannu ga tubabbun karuwan jihar a kalla guda dari biyar da saba’in da biyar 575.
Sana’o’i da ake koyawa karuwan tare da hadin guiwa da hukumar samar da ayyukan yi ta kasa NDE, sun hada da harkokin kasuwanci, Ilimin sarrafa kwamfuta, Gyaran kai, kitso, saka da kuma Dinki.
Sauran Sana’o’i da za’a cigaba da koyawa karuwan sun hada da Kwalliya, sana’ar hada abinci, kiwon kaji, kiwon kifi, hada takalma da jakka da dai sauransu.
Sannan kuma Hukumar ta yabawa karuwan da suka mika wuya daga wannan kazamar rayuwa ta bin maza sa sukw, wacce ke da hadarin gaske Duniya da Lahira.
Gwamnatin Bauchi ta kara da cewa, zata dauki dawainiyar aurar da tubabbun mata karuwan da zaran an kammala koyar dasu sana’o’i, sannan kuma Gwamnatin ce zata dauki duka hidimar auren da za’a musu sannan za’a sanar da karin bayani kan ranar daura auren.