Goodluck Jonathan Ya Yi Wa Al’umar Musulmin Najeriya Barka Da Sallah

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya taya al’umar musulmi Barka da Sallah da fatan Allah ya karbi ibadar Azumin da aka gabatar a watan Ramadan.

Tsohon shugaban ya wallafa Sakon Barka da Sallah ta shafinsa na facebook a safiyar litinin din nan, wadda ta zo daidai da daya ga watan Shawwal na shekarar hijira ta 1443.

Jonathan ya c, “Ina taya al’umar musulmi murnar kammala azumin watan ramadan, da fatan Allah ya karbi dukkan addu’o’in ‘yan uwa musulmi, kuma ya bamu albarkacin watan ramadan, albarkar kuma ta kasance tare da mu baki daya,”

“Muna fatan samun zaman lafiya, wadata da farin ciki a kowane fanni na rayuwa. Mu yi amfani da wannan dama mu rika tunawa da mabukata yayin da muke gudanar da bukukuwan Sallah da yin addu’o’in samun zaman lafiya a kasarmu.” Inji Jonathan.

Mutane da dama cikin mabiya ahafin tsohon shugaban sun bayyana far in cikinsu da ganin sakon na Barka da Sallah.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button